12 Agusta 2014 - 14:02
Gwamnatin Amurca Zata Bawa Kasar Liberia Maganin Ebola Na ZMapp A Wannan Makon

Gwamnatin kasar Amurca ta yi alkawarin mikawa kasar Leberia samfurin maganin Ebola na gwaji wanda ake kira ZMapp.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa gwamnatin kasar Liberia ta ce za’a kawo mata maganin cutar ta Ebola na gwaji a cikin wannan makon.

Kasar Liberia dai tana daga cikin kasar Africa ta yamma wadanda cutar ta kashe mutane sun fi dubu guda.

Maganin na gwaji wato ZMapp ya yi amfani a kan wasu likitoci amurcawa wadanda suka kamu da cutar a lokacinda suke kokarin taimakawa wadanda suka kamu da ita a kasar Liberia.

A halin yanzu dai cutar ta shafia kasashen Guinea Liberia Saliyo da Nigeria ne dukkaninsu a yammacin Africa. ABNA